
Hukumar kula da Zirga-zirgar Jiragen ƙasa ta Ƙasa, NRC, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan titin jirgin kasa na Abuja-Kaduna, sakamakon tsautsayi da jirgin ya yi a Kubwa, Abuja a jiya Juma’a.
Daraktan ayyuka na NRC, Niyi Alli, wanda ya yi nadamar matsalar da jirgin ya samu sakamakon jirkicewa da ya yi da ga kan layin dogo, ya nemi afuwar fasinjojin da aka soke tafiye-tafiyensu saboda lamarin a ranar Juma’a.
“Hukumomi a NRC na nadamar sanar da jama’a, musamman fasinjojinmu na AK3 da KA4 na yau 27 ga watan Junairu cewa haɗarin da aka samu a layinmu na jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ya faru ne sakamakon rashin layin KA4 a tashar Kubwa. .
“Ba a sami asarar rayuka ba. Muna matukar ba da hakuri ga fasinjojin da wannan lamari ya shafa.
“An tattara tawagar ceto ta NRC zuwa wurin don sake yin aikin gyaran hanyar. Sakamakon haka, an dakatar da jigilar jirgin kasa na Abuja Kaduna na wani dan lokaci.
“Yayin da aka tabbatar da fara aikin tun da wuri, duk rashin jin daɗi ga fasinjojinmu masu daraja na da matukar nadama,” in ji Mista Alli.
Daga nan sai darektan ya bayyana kudurin hukumar na tabbatar da bullo da wasu karin matakan aiki a fadin kasar don tabbatar da ayyukan jiragen kasa lafiya