
Rundunar ƴansanda a jihar Nasarawa ta tabbatar da ceto sauran ɗaliban makarantar Alwaza da ke karamar hukumar Doma da ke karamar hukumar Doma da aka sace kwanakin baya.
DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansandan jihar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiya Juma’a a garin Lafia.
Wasu ƴanbindiga ne su ka yi garkuwa da daliban makarantar ta Alwaza su shida tun a ranar Juma’a, 20 ga watan Janairu, da misalin karfe 7:00 na safe.
Idan dai za a iya tunawa, ƴansanda tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro da mafarauta ne su ka kubutar da biyu daga cikin daliban a ranar 21 ga watan Janairu, kwana guda bayan sace su.
Sai dai kuma PPRO ɗin ya ce da misalin karfe 7:00 na safiyar jiya Juma’a, tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa tare da hadin gwiwar mafarauta ne suka ceto ragowar daliban guda hudu lafiya lau a kauyen Doka da ke karamar hukumar Doma.
Kakakin ƴansandan ya kara da cewa an kai yaran asibiti domin duba lafiyarsu, sannan daga bisani a sada su da iyayensu.
Ya ce, Maiyaki Muhammad Baba, kwamishinan ƴansanda a jihar ya nuna godiya ga jama’a bisa goyon bayan da su ka bayar a tsawon lokacin binciken daliban.
Ya ce ko da yake ba a kama kowa daga waɗanda su kai garkuwa da yaran ba, ya roki jama’a da su taimaka wa ƴansanda da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin.