
Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulki, Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini da baƙin cikin kisan da a ka yi wa wasu mabiya darikar Tijjaniyya 19 da aka kashe a ƙasar Burkina Faso.
Rahotanni sun nuna cewa an kashe mutanen ne, waɗanda ƴan Nijeriya ne a ranar Laraba, a kan hanyar su ta zuwa ƙasar Senegal domin ziyara.
A wata sanarwa da mai taimakawa Tinubun a kan yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz ya sanyawa hannu a yau Lahadi, ɗan takarar shugaban ƙasar ya nuna baƙin cikin sa kan abinda ya faru.
“Wannan abin baƙi ciki ne a ce mutane basu ji ba basu gani ba za a tare su hanya a hallaka su kai tsaye. Dole ne a bi diddigin wannan magana domin bi musu haƙƙinsu,” in ji shi.
Tinubun ya kuma aike da saƙon ta’aziyya ga shugabannin ɗarikar Tijjaniyya da kuma iyalan waɗanda aka kashe a ƙasar Burkina Fason.
Tsohon gwamnan Legas ɗin ya kuma miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga dukkanin shugabannin Tijjaniyya na Nijeriya, da iyali da ƴan uwan mamatan.
“Ina kuma kira ga ma’aikatar ƙasashen waje ta ƙasa da ofishin jakadanci Nijeriya a Burkina Faso da su gaggauta bincike kan wannan al’amari domin ganin an hukunta waɗanda suke da hannu a ciki da kuma bi wa iyalan mamatan haƙƙinsu,” in ji shi.
Ya yi addu’ar Allah ya gafartawa waɗanda suka rasa rayukansu ya kuma ba wa iyalansu haƙurin jure rashin.