
An ceto wata mata da rai bayan ta makale a cikin ɓaraguzan ginin da ya ruguje sa’o’i 52 da suka gabata sakamakon wata mummunar girgizar kasa da ta afku a kudu maso gabashin Turkiyya.
Hotunan gidan talabijin na NTV a yau Laraba sun nuna ayyukan agajin gaggawa a lardin Kahramanmaraş da ke kusa da kan iyaka da Siriya, dauke da matar a kan gadon asibiti zuwa motar daukar marasa lafiya.
An ce an kubutar da matar, mai shekaru 58 a wani otal da ya ruguje.
Lardin Kahramanmaraş ya fuskanci girgizar kasar mai ƙarfi.
Girgizar kasar ita ce mafi karfi wacce ta kai ma’aunin mita 7.7 kuma ta afku da karfe 01:17 agogon GMT a ranar Litinin.