Home Labarai Gwamnatin Zamfara ta kori Kungiyoyi Masu Zaman Kansu daga jihar

Gwamnatin Zamfara ta kori Kungiyoyi Masu Zaman Kansu daga jihar

0
Gwamnatin Zamfara ta kori Kungiyoyi Masu Zaman Kansu daga jihar

Gwamnatin jihar Zamfara ta umurci dukkanin kungiyoyi masu zaman kansu, NGOs, da su fice daga jihar bisa zarginsu da ayyukan laifi.

Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Maman Tsafe ya fitar a jiya Talata.

Kwamishinan ya ce wannan umarni na nan-take ne.

A cewarsa, wasu kungiyoyi suna gudanar da ayyukansu ba bisa ka’ida ba, suna kuma gudanar da wasu ayyuka da ke haifar da rashin tsaro a jihar.

“An kuma lura cewa yawancin wadannan kungiyoyi masu zaman kansu ba bisa ka’ida ma ba su yi rajista da jihar ba bisa ka’idojin gwamnati da aka gindaya.

“An kuma gano wasu daga cikin su da aikata ayyukan da ke kara haifar da rashin tsaro a jihar da kuma makwabtanta.

“Daga yanzu, gwamnati na umurtar duk kungiyoyi masu zaman kansu a jihar da su tattara inasu-inasu su fice daga jihar nan take,” in ji Mista Tsafe.