Home Siyasa Zan yi maganin zaman kashe-wando idan na ci zaɓe– Obi

Zan yi maganin zaman kashe-wando idan na ci zaɓe– Obi

0
Zan yi maganin zaman kashe-wando idan na ci zaɓe– Obi

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ne ya yi alkawarin magance zaman kashe wando tare da farfado da sana’o’i musamman a tsakanin matasan kasar nan muddin ya dare karagar Shugabancin Najeriya a 2023.

Ya bayyana haka ne a jiya Litinin a Fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya a Jihar Kaduna, lokacin da ya jagoranci wata tawagar jiga-jigan jam’iyyar wajen kai gaisuwa ga Sarki Ahmad Nuhu Bamalli.

Dan takarar, wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra ne ya ce harkar noma ma za ta samu tagomashi domin ita ce babbar sana’ar da za ta taimaki a’’umma da kasa baki daya.

Ya ce Arewacin Najeriya na da kyakkyawan yanayi da kuma fadin kasa mai yalwa wanda idan aka samar da ingantaccen tallafi ga manoma, Najeriya za ta yi tunkaho da noma.

Obi wanda mataimakin takararsa, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya yi wa rakiya, ya shawarci ’yan Nijeriya da su guji siyasar kabilanci da bangaranci da kuma addinanci.