Home Ƙasashen waje Ana shirin haramta TikTok a Amurka

Ana shirin haramta TikTok a Amurka

0
Ana shirin haramta TikTok a Amurka

Fadar gwammnatin Amurka ta ce tana goyon-bayan wani ƙudirin doka na gamayar jam’iyyun siyasar ƙasar biyu da zai bai wa Shugaba Biden ƙarfin haramta amfanin da shafin TikTok na China da sauran wasu fasahohin ƙasashen ƙetare da za su kasance barazana ga tsaron ƙasar.

BBC ya rawaito cewa, mataimaki na musamman kan harkar tsaron Fadar White House Jake Sullivan ya ce ƙudurin zai bai wa gwamnatin Amurka damar kare kanta daga kutsen wasu gwamnatocin.

Ƙudirin daI ya samu amincewar gwamman ‘yan jam’iyyun Democrats da Republican a majalisar dattijai.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a nan Nijeriya babu wani yunkuri da gwamnatin ƙasar ke yi na kula da harkokin TikTok, duk da cewa masu amfani da ita na wuce gona da iri.

Ko a kwanan nan ma sai da wata kotun shari’ar Muslunci ta yanke wa wasu ƴan TikTok, ciki har da shahararriyar jarumar TikTok, Murja Kunya, hukunci.