Home Siyasa SIYASA BA DA GABA BA: Magoya bayan Abba Gida-Gida da Gawuna sun shirya wasan ƙwallon ƙafa a Kano

SIYASA BA DA GABA BA: Magoya bayan Abba Gida-Gida da Gawuna sun shirya wasan ƙwallon ƙafa a Kano

0
SIYASA BA DA GABA BA: Magoya bayan Abba Gida-Gida da Gawuna sun shirya wasan ƙwallon ƙafa a Kano

Wasu matasa a jihar Kano sun shirya wasan sada-zumunci na ƙwallon ƙafa tsakanin magoya bayan zaɓaɓɓen gwamna, Abba Kabir Yusuf da kuma na abokin hamayyar sa, Nasiru Yusuf Gawuna.

Freedom Radio ta rawaito cewa matasan sun yanke shawarar shirya wasan ƙwallon ƙafar ne a unguwar Hausawa, Ƙaramar Hukumar Tarauni, domin nuna cewa “siyasa ba gaba ba ce”.

Adamu Maisalati Hausawa, ya shaida wa Freedom cewa sun shirya wasan ne domin wanzar da zaman lafiya tsakaninsu, duk d a cewa akwai bambancin ra’ayi na siyasa.

“Mun shirya wannan wasan ne domin wanzar da zaman lafiya tsakanin mu domin akwai rayuwa bayan zaɓe. Mun shirya wasan ƙwallon ƙafar ne domin mu kara dankon zumunci tsakanin mu tare da habbakar arziki a yankin mu,” in ji Hausawa.

Ya kuma yi kira ga sauran unguwanni a jihar da su ma su ɗauki gaɓaran ƙoƙarin zama lafiya da juna ba tare da gaba ta siyasa ba.

Ya ƙara da cewa za a yi wasan ne a yau Laraba a Makarantar Ado Gwaram da misalin ƙarfe 4 na yamma.