Home Labarai Kungiyar daliban Arewa maso gabas sun karrama Sheikh Bala Lau

Kungiyar daliban Arewa maso gabas sun karrama Sheikh Bala Lau

0
Kungiyar daliban Arewa maso gabas sun karrama Sheikh Bala Lau

Daga Mahmud Isa Yola

Kungiyar Dalibai ta Northeast Students Peace Initiative’ ta karrama shugaban kungiyar Izala na tarayyar Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau da lambar yabo akan son Zaman lafiya.

Da yake jawabi, shugaban kungiyar yace sun zabi Sheikh Bala Lau ne saboda kokarin sa na son zaman lafiya a tarayyar Nijeriya. Ya misalta Shehin malamin da ginshiki na zaman lafiya da son cigaban ilimi.

Kungiyar ta dalibai tayi tattaki har zuwa gidan Sheikh Bala Lau dake Yola, ta danka mishi lambar yabon.

Sheikh Bala Lau yayin da yake tarban tawagar ya gargadi daliban da su kasance jakadun musulunci a duk inda suka samu kan su.

Yace wajibi ne su fifita ilimi kuma su tsaya su neme shi da gaske, saboda ilimi shine gishirin rayuwa.

Shehin malamin yace zaman lafiya abu ne da ya kamata a samu a wurin duk wani musulmin kwarai. Yace tashin hankali da tayar da zaune tsaye ba na musulmi bane balle malami.