
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce ta kama mutane 352 tare da kama tan 2.1 na miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Kwamandan NDLEA a jihar, Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a Kano a yau Alhamis.
Ahmad ya ce an kama mutanen ne a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Ya ce wadanda ake zargin sun hada da maza 208 da mata 44, yayin da ƙwayoyin da aka kama sun hada da kilogiram 955.304 na tabar wiwi, da Codeine da Tramadol kilogiram 1,225.05.
Sauran, a cewarsa, sun hada da gram 25 na hodar iblis, gram 17 na ƙwayar heroin da kuma gram 52 na methamphetamine.
Kwamandan ya ce babban kalubalen da ke gaban hukumar a jihar shi ne shawo kan al’umma wajen bankado masu sayar da miyagun kwayoyi a tsakaninsu.