Home Labarai Yadda wani Faston boge ya tsere da wayoyi 52 da kuɗaɗe bayan taron addu’ar kiristanci a Ibadan

Yadda wani Faston boge ya tsere da wayoyi 52 da kuɗaɗe bayan taron addu’ar kiristanci a Ibadan

0
Yadda wani Faston boge ya tsere da wayoyi 52 da kuɗaɗe bayan taron addu’ar kiristanci a Ibadan

A yanzu haka mazauna unguwar Aponrin da ke unguwar Agbowo a garin Ibadan sun nadama neman wani Fasto da ake zargin ya tsere da wayoyin Android da iPhone guda 52 da kudi da wasu kayayyaki masu daraja na mahalarta bayan sun shafe kwanaki uku suna tafka addu’o’i na kiristanci.

An ce faston ya shaida wa wadanda abin ya shafa cewa da ikon Ubangiji ne ya zo Ibadan daga ƙasar Gambiya domin ya gabatar musu da taron addu’o’in.

Faston, a ranar karshe na taron, ya yi ikirarin cewa Ruhi Mai Tsarki ne ya umurce shi da ya gaya wa wadanda suka halarci taron su mika wayoyinsu, kudadensu da sauran kayayyaki masu daraja gare shi.

Ai kuwa sai ya tsere da waɗannan kayayyaki.

Wadanda abin ya shafa sun ce Faston, wanda ya yaudare su cikin kwanaki uku na azumi da addu’o’i, ya tsere a ranar karshe kuma duk kokarin gano inda yake ya ci tura.

Wata mata da abin ya shafa mai suna Grace Akintola ta ce da yawa daga cikin matan da mazansu suka mutu sun halarci taron ne saboda faston ya yi alkawarin bai wa kowannen su buhun shinkafa da kudi.

Akintola, wacce bazawara ce ta bayyana cewa Faston ya kuma yi alkawarin baiwa mahalarta taron addu’ar kyaututtuka da tallafin karatu.

“Ranar karshe ta taron, shi ( Fasto) ya sayar mana da ruwan kwalaba a kan kudi N4,800; ya ce an hada ruwan ne da turare kuma mutane da yawa sun biya shi sun karba,” inji ta.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya aike wa NAN.

Osifeso ya ce an fara gudanar da bincike kan lamarin kuma za a yi karin bayani nan gaba