Home Labarai An jefe wani direba ya mutu bayan ya kashe wasu mutum 2 da mota a Ondo

An jefe wani direba ya mutu bayan ya kashe wasu mutum 2 da mota a Ondo

0
An jefe wani direba ya mutu bayan ya kashe wasu mutum 2 da mota a Ondo

Wasu fusatattun matasa a yau Litinin, sun jefe wani mutum mai shekaru 35 da duwatsu har lahira bisa zargin sa da kashe mutane biyu tare da raunata wasu 6 a wani haɗarin da ya afku a hanyar Ijoka, Akure, babban birnin jihar Ondo.

Kakakin rundunar yansandan jihar Ondo, SP Olufunmilayo Odunlami Omisanya, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.

Omisanya ta ce haɗarin ya hada da wata mota da babur ɗin acaɓa.

“Akwai haɗarin da ya yi sanadin mutuwar wani direban babur, kuma maimakon mutanen da ke kusa da su su taimaka su ceci waɗanda haɗarin ya shafa, sai suka yi kan direban ta hanyar kashe matashin tare da kona motarsa,” inji ta.

Kakakin ƴansandan ta ci gaba da cewa, amma da gaggawar zuwa sa ƴansandan suka yi, da an kashe iyayen direban su ma.

Ta ce iyayen ba sa cikin motar da dan nasu ke tukawa, amma sun zo wurin ne kawai don ganin abin da ke faruwa.

“A gaba ɗaya, an tabbatar da mutuwar mutane biyu yayin da wasu shidan da suka samu raunuka a hatsarin a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti,” in ji PPRO.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya tattaro cewa ana zargin direban cewa dan damfara ta intanet ne, wanda aka fi sani da ‘Yahoo boy’.