Home Labarai Likitoci sun yi nasarar raba tagwaye ƴan Nijeriya da aka haifa a manne

Likitoci sun yi nasarar raba tagwaye ƴan Nijeriya da aka haifa a manne

0
Likitoci sun yi nasarar raba tagwaye ƴan Nijeriya da aka haifa a manne
In implementation of directives of King Salman, Nigerian conjoined twins Hassana and Hasina underwent separation surgery by a medical team of 35 specialists in Riyadh

An yi nasarar raba wasu tagwaye ƴan Najeriya, Hassanah da Hasina da aka haifa a manne, bayan an shafe sa’o’i 14 ana aikin rabawar a kasar Saudiyya.

An haifi tagwayen a ranar 12 ga Janairu, 2022, a Kaduna, Hassana da Hassina, inda aka haife su da ƙashin ƙugu, hanta, hanji, da kuma wajen yin fitsari da bahaya guda ɗaya.

Kamfanin dillancin labarai na Arab News ya rawaito cewa, tawagar kwararrun likitocin mai mutum 85 ta yi nasarar kammala matakai bakwai daga cikin takwas na aikin raba tagwayen a asibitin kwararru na yara na Sarki Abdullah.

A ranar 9 ga watan Nuwamban 2022 ne aka kai tagwayen da iyayensu birnin Riyadh a jirgin sama, bisa amincewar Sarkin, wanda ya dauki nauyin aikin a madadin masarautar Saudiyya.

Kafin a fara aikin, shugaban tawagar likitocin, Dr Abdullah Al-Rabeeah, mai ba da shawara ga kotun masarautar Saudiyya kuma babban mai kula da agajin jin-kai na cibiyar agaji ta Sarki Salman ya ce aikin zai kunshi matakai takwas.

A baya dai ayyukan jin kai na Saudiyya sun taimaka wa tagwaye guda 130 daga kasashe 23 a tsawon shekaru 33, kuma Hassana da Hassina za su kasance na 56 na tagwayen da su ka ci gabiyar aikin raba wa.

Jakadan Najeriya a Saudiyya, Yahaya Lawal, ya gode wa shugabannin masarautar bisa irin taimakon da suka yi wa wadannan tagwayen da aka haifa a manne.