Home Labarai May 29: SSS sun bankaɗo shirin daƙile rantsar da shugabanni

May 29: SSS sun bankaɗo shirin daƙile rantsar da shugabanni

0
May 29: SSS sun bankaɗo shirin daƙile rantsar da shugabanni

Hukumar Ƴansandan Farin Kaya, SSS, ta ce ta bankaɗo wani shiri da wasu batagari ke yi na kawo naƙasu wajen bikin rantsuwa da sauran shirye-shirye na siyasa a fadin ƙasar nan.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Dakta Peter Afunanya ne ya bayyana haka a wata sanarwa danya fitar a yau Alhamis a Abuja.

A cewar sa, shirin da ɓata-garin ke yi na yunkurin dakile kokarin jami’an tsaro na samar da zaman lafiya a kasar ne ta yadda za su haifar da tsoro da fargaba a zukatan yan ƙasa.

“Sabo da haka mu ma jan hankalin ƴan kasa, kafafen yaɗa labarai da kungiyoyi masu zaman kansu da su bi matakan tsaro da aka sanya a yayin tarukan.

“Haka kuma muna kira gare su da su gujewa duk wasu labaran kanzon kurege, raɗe-raɗi da jita-jita, tare da gujewa yin labarai na karin gishiri don kawo rarrabwar kai a kasa,” in ji shi.