
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na kawar da tallafin man fetur wanda ya ce zai ceto kasar nan a lokacin rikicin tattalin arziki.
Tinubu ya yi wannan yabo ne a yayin jawabinsa na farko bayan rantsar da shi da alkalin alkalan Nijeriya, Mai shari’a Kayode Ariwoola ya yi a dandalin Eagles Square da ke Abuja.
Ya ce: “A maimakon haka, za mu karkatar kudaden zuwa mafi kyawun ayyukan ci gaba da suka haɗa da ilimi, kiwon lafiya da ayyukan yi da za su inganta rayuwar miliyoyin yan Nijeriya.”
Tinubu ya ce manufar hada-hadar kudi ta Najeriya na bukatar tsaftacewa kamar yadda ya bukaci Babban Bankin Najeriya ya yi aiki wajen samar da harkar kuɗaɗen waje ta bai-ɗaya.
“Wannan zai sanya a yi amfani da kudaden da ake samu ta wannan ɓangaren wajen saka hannun jari mai ma’ana don farfaɗo da tattalin arzikin kasa .”