Home Labarai Ƴan bindiga sun sace shugabannin mata na APC su biyu bayan sun dawo daga rantsar da Uba Sani

Ƴan bindiga sun sace shugabannin mata na APC su biyu bayan sun dawo daga rantsar da Uba Sani

0
Ƴan bindiga sun sace shugabannin mata na APC su biyu bayan sun dawo daga rantsar da Uba Sani

Wasu yanbindiga da ake kyautata zaton ƴan fashin jeji ne sun yi garkuwa da wasu shugabannin mata biyu na jam’iyyar APC a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce an yi garkuwa da matan ne a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari yayin da su ke komawa gida bayan halartar bikin rantsar da Gwamna Uba Sani a ranar Litinin.

Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin Gwari, BEPU, Ishaq Usman, ya shaida wa Daily Trust a jiya Laraba cewa lamarin ya faru ne a unguwar Manini da ke kan hanyar.

A cewarsa, yan bindigar sun tare hanya tare da yin garkuwa da wadanda matan da kuma wasu matafiya a ranar Talata.

Matan sun hada da shugabar mata ta APC a Birnin Gwari, Lami Awarware, da mataimakiyarta Haulatu Aliyu.

Har yanzu dai masu garkuwa da mutanen ba su tuntubi iyalan matan ba.

Har ila yau gwamnatin jihar da hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar, PPRO, Mohammed Jalige, ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan lamarin ba.