Home Labarai FCTA za ta samar da titunan keke a Abuja

FCTA za ta samar da titunan keke a Abuja

0
FCTA za ta samar da titunan keke a Abuja

Olusade Adesola, sakataren dindindin na hukumar babban birnin tarayya, FCTA, ya ce za a dau matakai na samar da titunan keke a cikin babban birnin tarayya Abuja.

Adesola ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Sadarwa na FCT, Muhammad Sule, ya fitar a Abuja a yau Lahadi.

A cewar sanarwar, Mista Adesola ya yi magana ne a wajen bude bikin ranar keke ta duniya ta 2023 a Abuja.

Ya ce dama can an riga an fitar da hanyoyin keke a tsarin fitar da Abuja, inda ya kara da cewa yanzu sai dai a yi aikin gina hanyoyin.

“Wannan matakin zai zurfafa kamfen don rage tasirin sauyin yanayi, za a rage fitar da hayaki a ababe hawa idan aka karfafa hawa keke,” in ji shi.