
Ba wai sabon abu ba ne cewa takarar shugabancin majalisar dattawa ta Akpabio da Barau ta samu karɓuwa daga ɓangarori da dama. Tun daga kan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Kassim Shettima da kuma gwamnoni a jam’iyya mai mulki da ma jam’iyyun adawa kamar su Gwamna Yahaya Bello na Kogi da ma tsohon gwamna Nyesom Wike na Rivers da sauransu.
Yayin da ake ta alla-alla a yi zaben majalisa ta goma, tarihin Sanata Godswill Akpabio ba boyayye ba ne duba da cewa tsohon gwamna ne na Akwai Ibom kuma tsohon Ministan Ma’aikatar kula Da Neja-Delta, yayin da abokin takarar sa Barau Jibrin ya kasance gogaggen ɗan siyasa.
Haifaffen cikin birnin Kano, Barau ya yi digiri a fannin ilimin akawu sannan ya yi digiri na biyu a fannin sarrafa kudade da fitar da farashi, da digiri na biyu a ilimin gudanarwa da kuma digiri na biyu a harkar gudanar da kasuwanci (MBA), sannan ya samu shaidar digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci a Jami’ar Cornell da ke Amurka.
Tsohon Shugaban Kamfanin Zuba Jari da Kaddarori na Jihar Kano, kuma Kwamishinan Kimiyya da Fasaha a Jihar, ƙarfin hidimtawar Barau ga al’ummar mazabarsa ne ya zaburar da shi tsayawa takarar dan Majalisar Wakilai ta Tarayya a mazabar Tarauni ta Jihar Kano a zaben 1999, wanda ya kuma yi nasara.
Bayan ya yi zango ɗaya a majalisar wakilai, sannan ya yi zango uku a majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya tara dimbin kwarewa mai zurfi, wanda ya sanya shi kan matsayi wanda shi kaɗai ke da shi. Hasali ma, a halin yanzu, shi ne zababben Sanata mafi kwarewa a yankin Arewa-maso-Yamma da kuma Jihar Kano, wanda ya ke a cikin zango na hudu, wanda ya kawo ƙudirori da dokoki sakamakon gogewar da ya ke da ita da babu mai irin ta.
Kwanan nan, Progressive Youth Intellectuals tare da haɗin gwiwar Youths Digest, masu shirya taron shekara-shekara na bayar da lambar yabo ta aikin jarida na Campus su ka nuna goyon bayan su ga Sanata Barau bisa nuna kwarewa da gaskiya a cikin ayyukan da ya yi a zauren majalisa, musamman a kan ilimi, kwarewa da kuma bunkasa matasa.
Bisa ɗumbin nasarori da ya samu a Majalisar Dokoki ta kasa sama da zango hudu ne ya sanya masu fafutukar ci gaban matasa na ganin ya dace a zabi Barau Jibrin, dan takara daga shiyyar Arewa-maso-Yamma, a matsayin mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Jibrin, a lokacin da yake zaman majalisar wakilai, ya jagoranci kwamitin kasafin kudi na majalisar kuma ya kasance mamba a kwamitin kula da wutar lantarki na majalisar. A zamanin wakilcin sa, ya nuna kwazonsa da ya shahara wajen bai wa ilimi fifiko, musamman ga matasa, ta hanyar ci gaba da fafutukar kare muradun matasan Nijeriya.
Ya kasance mai goyon bayan kudirin dokar gina Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Bichi a Jihar Kano. Sannan kuma ya dauki nauyin kudirin kafa makarantar kimiyya ta tarayya ta Kabo.
Sanata Jibrin ya kuma gabatar da wani kudirin doka a 2020 don samar da hukumar raya yankin Arewa-maso-Yamma domin magance gibin ci gaban ababen more rayuwa a yankin.
Duk da dimbin sanatoci masu nagarta a yankin, Sanata Barau ya samu kyautar gwarzon dan majalisar dattawan Najeriya a 2017. Nasarar da ya samu ta tabbatar da ayyuka daban-daban na samar da zaman lafiya da ci gaban kasa, inda wannan tagomashi ya sanya aka bashi lambar girma ta ƙasa mai taken GCON.
Ya kuma taka rawar gani sosai a ayyukan raya kasa da dama a lokacin da ya ke a kwamitin raya yankin Neja Delta, masana’antu, sufuri da kwamitocin kula da kasafi.
Ko a zaben shugaban kasa na 2023, Sanata Barau ya nuna ƙarfinsa da farin jininsa. Jihar sa, Kano ce ta samu kuri’u na biyu a yawa jam’iyyar APC. Sannan kuma, mazaɓar Sanata Barau ta Arewacin Kano ce ta samu kusan rabin kuri’u (dubu 200) na kuri’u 513,000 da jam’iyyar APC ta samu a jihar.
A ci gaba da nazarin sakamakon zaben, an gano cewa mahaifar Sanata Barau, wato yankin Arewa maso Yamma, ita ce ta samar da mafi yawan kuri’u na jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2023, wanda ya kai kuri’u miliyan 2.7.
Hakazalika, duk da guguwar jam’iyyar New Nigerian People’s Party, NNPP a jihar Kano, Sanata Barau Jibrin ne kaɗai da ya tsaya kyam a APC da guguwar ba ta taɓa ba, inda ya yi nasarar lashe zabensa na sake komawa majalisar dattawa. Wannan yana nuni da gaskiyar cewa Sanatan ya na yi wa al’ummarsa abin da ya dace.
Sanata Barau Jibrin ya ci gaba da gina siyasar sa a shekaru masu zuwa, inda ya lashe zaben majalisar dattawan tarayyar Nijeriya a 2015, mai wakiltar Kano ta Arewa a dandalin jam’iyyar All Progressives Congress. Ya sake maimaita wannan nasara a 2019 da 2023, inda ya lashe zabukan majalisar dattawa.
Daga karshe, kyawun halayen Sanata Barau Jibrin da kuma amanar sa ce ta sanya ya ke dambin masoya. Halayyar sa da martabar sa ce ta sa ya fito a matsayin shugaban da za a iya dogaro da shi wajen aiwatar da maslahar al’ummar Najeriya. Wannan ya banbanta shi a matsayin ginshiƙi mai ƙwari a zamanin da amincewa da jami’an gwamnati ke da muhimmanci.
Don haka, tsayawa takarar Sanata Barau Jibrin a matsayin mai girma mataimakin shugaban majalisar dattawa a majalissar ta 10 ta tarayyar Najeriya ta zama wani haske ga al’ummar kasar nan. Goyon bayan Hasashen Matasa Masu Hankali, tare da jajircewar Jibrin na ganin an samu sakamako mai ma’ana da kuma yaki da cin hanci da rashawa ne ya tabbatar da matsayinsa a matsayin zabin da ya dace da wannan muhimmiyar rawar.
Zaben Sanata Barau Jibrin CON a matsayin mataimakin Sanata Akpabio a kan kujerar shugabancin majalisar dattijai, ko shakka babu zai share fagen samun ci gaba da ba a taba ganin irinsa ba a Nijeriya a matsayin hadin kai. Sun tabbatar da cewa su shuwagabanni ne da ke da ikon jagorantar babban zauren majalisar a cikin lokacin “sabon fata” ga daukacin kasar.
Saajid Ibrahim, mai sharhi kan al’amuran jama’a ne ya rubuto daga Abuja.