
Masanin ilimin dabbobi, Farfesa Moshood Mustapha na Sashen nazarin dabbobi na Jami’ar Ilorin, ya bukaci ƴan Nijeriya da su rungumi noman kwadi domin samun ci gaban tattalin arziki.
Mustapha ya yi wannan kiran ne a yau Alhamis a garin Ilorin a cikin wata maƙala da ya gabatar a wani taron lacca na jami’ar, karo na 210, mai taken: “Man-made Lakes: A Means of Eradicating Man-made Poverty”.
Ya bayyana cewa, saboda ƙaruwar tsadar kiwon kifin da kuma kwararowar kwaɗi, jinsin Hoplobatrachusccipitalis daga dazuzzuka a Najeriya, noman wadannan kwadi ya zama wajibi.
“Mu na duba yiwuwar rainon kwado tun daga matsayin ɗan-yanɗo har zuwa ya balaga ya zama cikakkiyar halitta.
“Tunda kwadi na rayuwa a cikin ruwa, nasarar noman su zai dogara ne akan ingancin ruwan tafki da ake kiwon su,” in ji shi.