Home Labarai Gwamnatin Jigawa ta kai ƙorafi ga EFCC da PCACC cewa gwamnatin Kano ta sayar da gidaje da filayenta

Gwamnatin Jigawa ta kai ƙorafi ga EFCC da PCACC cewa gwamnatin Kano ta sayar da gidaje da filayenta

0
Gwamnatin Jigawa ta kai ƙorafi ga EFCC da PCACC cewa gwamnatin Kano ta sayar da gidaje da filayenta

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bukaci Hukumar Yaki da Cin-hanci da Rashawa, EFCC da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, da su binciki halin da wasu kadarorin da ta samu a lokacin da aka cire Jihar daga Kano a 1991.

A wasu wasiku daban-daban dauke da sa hannun kwamishinan ayyuka na musamman na jihar, Auwal Sankara, gwamnatin ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da su tantance matsayin filaye biyu da gidajen GP [Gwamnati] guda shida a cikin jihar ta Kano.

Yayin da ya ke koka wa da jinkirin samun kadarorin, Mista Sankara ya ce kokarin da gwamnatocin baya suka yi na kwato kadarorin ya ci tura.

Ya ce: “Kamar yadda kuka sani, an samar da Jihar Jigawa daga tsohuwar Jihar Kano a 1991. Bayan da aka kirkiro Jihar Jigawa, an yi wani shiri na raba kadarori tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Jihar Jigawa.

“Duk da haka, abin takaici ne ganin yadda batun rabon kadarorin ya dauki tsawon lokaci, duk da kokarin da jihar Jigawa ta yi na warware matsalar cikin ruwan sanyi.

“A dangane da haka, ina mai jan hankalin ku ga kadarorin da har yanzu a ke tirka-tirka a kan su kuma mu na bukatar ku shiga tsakani.

“Kadarorin da ake magana a kai sun hada da fil mai lamba 133 na TP/UDB/173 a Farm Centre, da kuma gidajen GP da aka ware wa jihar Jigawa: GP 447 Suleiman Crescent, GP 897 Maiduguri Road, GP 982 Maiduguri Road, GP 891 Maiduguri Road, GP 827 read the Sokoto Road, GP 827 read the Sokoto Road, GP 827 the Sokoto Road, GP 827 read the Sokoto Road, 827 road,” a cewar wasikar.