Home Labarai Kotu ta bada belin Emiefele

Kotu ta bada belin Emiefele

0
Kotu ta bada belin Emiefele

Mai shari’a Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke Legas a yau Talata ya bada belin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a kan kudi naira miliyan 20.

Ana tuhumar Mista Emefiele ne kan tuhume-tuhume biyu da suka hada da mallakar bindiga guda daya, da kuma mallakar harsasai 123 ba tare da lasisi ba.

Sai dai ya musanta zargin da ake masa.

Lauyan wanda ake kara, Joseph Daudu, SAN, wanda ya jagoranci wasu manyan lauyoyi hudu, ya sanar da kotun bukatar neman belin wanda ake kara.

Sai dai mai gabatar da kara, N.B Jones, ya ki amincewa da neman belin da aka yi bisa hujjar cewa ba a ba ta kwafin takardar ba.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Oweibo ya bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira miliyan 20 tare da mutane biyu da za su tsaya masa masu wannan adadi na kuɗi

Kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba.