
Kansiloli takwas a cikin goma sha ɗaya sun dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano, Auwalu Lawan Aronposu daga aiki har sai baba-ta-gani.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa dakatarwar ta Aranponsu na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun kansiloli 8 cikin 11 na majalisar da suka rattaba hannu kan dakatar da Ciyaman din.
Kansilolin sun umarci Ciyaman ɗin da ya mika ragamar shugabancin ga mataimakinsa, Hon. Muazu Abubakar Adamu kafin a kammala bincike.
A cikin wasikar dakatarwar da aka baiwa ‘yan jaridu a jiya Talata, kansilolin sun zargi Aranponsu da mika ragamar karɓar kudaden harajin na karamar hukumar kacokan wani ga abokinsa na ƙut-da ƙut da kuma gaza aiwatar da ayyukan ci gaban al’umma a Karamar Hukumar.
Hakazalika kansilolin sun zargi Ciyaman ɗin da almubazzaranci da kudade, rashin zuwa aiki, son zuciya, rashin da’a da kuma karya dokokin majalisar da dai sauransu.
Kazalika, yan majalisar sun zargi shugaban da karkatar da wasu kuɗaɗe da aka fitar da su don siyan motocin karamar hukumar, sannan sun zarge shi da yin katsalandan a cikin harkokin majalisar, wanda hakan ya haifar da rudani, hargitsi da zagon kasa.
Sai dai kuma Ciyaman ɗin ya musanta zarge-zargen, inda ya ce siyasa ce kawai domin tun da ba su taso da maganar ba sai yanzu.
Aronposu ya kuma ce ba a kai masa takardar dakatarwar ba hannu da hannu ba, sai dai ya ganta ne a shafukan sada zumunta.