
Majalisar dokokin jihar Kaduna a jiya Talata, ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi uku bisa zargin karkatar da kudaden da aka ware domin gudanar da ayyuka a yankunansu.
Shugabannin kananan hukumomin uku sun hada da Mathias Siman, PDP, Kaura, Nasara Rabo, APC, Kagarko, da Salasi Musa, PDP, Chikun.
Matakin dai ya biyo bayan gabatar da rahoton bincike kan harkokin kudi na shugabannin kananan hukumomi biyar da aka gabatar wa majalisar tun da fari.
Rahoton, wanda shugaban kwamitin wucin-gadi, Munira Tanimu (Mazabar Lere Gabas – APC) ta gabatar, ya samu amincewar majalisar gaba daya.
Misis Tanimu ta yi zargin cewa shugabannin da abin ya shafa ba su bi ka’idojin da suka dace ba wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, kamar yadda yake a sashe na 35 (23) na dokar hadahadar kuɗaɗen gwamnati ta jihar Kaduna, ta 2016.
An dakatar da shugabannin uku na tsawon watanni shida, kafin a ci gaba da gudanar da bincike, yayin da takwarorinsu na Birnin Gwari da Soba da aka wanke su daga aikata badaƙalar kuɗaɗe kuma za su ci gaba da rike kujerunsu.
An umurci shugabannin ƙananan hukumomin da aka dakatar da su fice daga ofisoshinsu tare da mikawa mataimakan su ragamar mulki.