
Farfesa Yusuf Usman, tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya, NHIS, ya yi kira da a kwata-kwata a hana sayar da maganin tari mai ɗauke da sinadarin Codeine a Nijeriya.
Farfesa Usman ya yi wannan kira ne yayin da ya ke gabatar da maƙala a taron wayar dakai kan illar shan miyagun ƙwayoyi mai taken; Shan miyagun ƙwayoyi da lalacewar tarbiyya, wanda Initiative for Community Action Against Drug Abuse, tare da haɗin gwiwar Coalition of Northern Group, CNG, su ia shirya a Kano a yau Laraba a hatabar Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano.
A cewar Farfesa Usman, waɗannan magunguna da ake sayar wa su ne masu ƙara gurɓata tarbiyyar matasa a cikin al’umma.
Ya yi kira ga ƴansanda, ƴan Hisbah da sauran jami’an tsaro da iyaye da malamai da a tashi tsaye wajen yakar mahaifar shaye-shaye.
A cewar sa, lokaci yayinda za a deba wani zarge-zargen cewa laifin wasu ne, inda ya ce “masu kawo ƙwayoyin nan an san su, masu sayarwa ma an san su haka masu sha ma an san su, to sai mu tashe tsaye minti maganin abun, kada mu tsaya wai sai dai gwamnati ta yi mana maganin mahaifar nan.”
Ya kuma kara da cewa zuwan su dazuzzukan wasu jihohi a arewacin Nijeriya tare da Sheikh Ahmad Gumi ya sanya su ka tabbatar da cewa ƴan ta’adda da aikata laifukan ne a ƙarƙashin zugar ƙwayoyi.
Ya ce idan dai ana son a samu ingantacciyar al’umma, to dole a tashi tsaye a yaki shan miyagun ƙwayoyi.