Home Labarai Bazoum ya ci alwashin kare dimokuraɗiyya bayan an masa juyin-mulki

Bazoum ya ci alwashin kare dimokuraɗiyya bayan an masa juyin-mulki

0
Bazoum ya ci alwashin kare dimokuraɗiyya bayan an masa juyin-mulki

Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya yi amfani da kafar sada zumunta ta yanar gizo a yau alhamis tare da shan alwashin kare kimar dimokiradiyya, kwana daya bayan hambarar da gwamnatin sa a wani juyin mulkin da sojoji suka yi.

Ministan harkokin wajen kasar, Hassoumi Massoudou shi ma ya fitar da wani sako a dandalin X, wanda aka fi sani da Twitter, domin “dukkan masu ra’ayin dimokaradiyya da masu kishin kasa” su bada gudunmawa kan juyin mulkin ya samu tasgaro.

Bayanin nasu ya biyo bayan wani jawabi ne da daddare da sojoji suka yi a jiya Laraba a gidan talabijin na kasar, inda suka sanar da cewa an tsige Bazoum daga kan karagar mulki, kuma an dakatar da dukkan hukumomin jamhuriyar, wanda ke zama juyin mulki karo na bakwai a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka tun 2020.

Tun da fari, a jiya Laraba jami’an tsaron fadar shugaban kasar su ka karɓe ikon fadar shugaban kasar da ke Yamai, babban birnin kasar tare da tsare Bazoum a ciki.

Wannan ya haifar da damuwa a yankin da ma duniya game da rashin zaman lafiya a kasar da ke zama babbar abokiyar kawance ga kasashen yammacin Turai da ke taimakawa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.

Har yanzu ana tsare da Bazoum a cikin fadar shugaban kasar da safiyar Alhamis, Massoudou ya fada a wata hira da kafar yada labaran Faransa ta France 24.

Sai dai kuma ba a san inda ministan yake ba.

Yamai ta yi rsit da sanyin safiyar yau Alhamis, yayin da ƴan kasar suka farka da labarin rufe kan iyakokin kasar da dokar hana fita da sojoji suka kafa a fadin kasar.