
Kungiyar Kwadago ta Ƙasa, NLC, ta ce za ta kira yajin aiki a duk fadin kasar a ranar 2 ga watan Agusta, idan gwamnatin tarayya ta gaza sauya manufofin masu tsauri da ta ɓullo da su, da su ka haɗa da cire tallafin man fetur.
Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwar Bayan taro mai ɗauke da sa hannu na hadin-gwiwa tsakanin shugaban kungiyar na kasa, Joe Ajaero, da Sakatare-Janar, Emmanuel Ugboaja, a karshen taron kwamitin tsakiya na ranar Talata.
A cewar sanarwar, ƙungiyar ta lura cewa ƴan Nijeriya sun rasa kwanciyar hankali sakamakon kalaman “tallafin mai ya tafi” da Shugaba Bola Tinubu ya yi a lokacin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Kungiyar ta NLC ta kuma ce gwamnati ta nuna rashin girmamawa da raini ga al’ummar Najeriya tare da gayyatar rashin jituwa tsakanin ta da ma’aikata da talakawan Najeriya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Kwamitin aiki na NLC na tsakiya ya lura cewa Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin kulawa da raini ga jama’ar Najeriya da ma’aikata da suka yi aiki kuma suka ci gaba da aiki ba tare da la’akari da jin daɗi da kukan ‘yan ƙasa ba.
“Da alama wannan gwamnatin ta shelanta yaki da cin hanci da rashawa a kan ma’aikata da talakawan Najeriya ba tare da wata kulawa ba ta bar su cikin halin rashin bege da rashin taimako; Gwamnatin tarayya ta ki sanya matakan kariya domin kare ‘yan Najeriya daga halin kuncin tattalin arziki da manufofinta suka jefa jama’a a maimakon haka ta yanke shawarar cin mutuncin hankalin talakawan Najeriya ta hanyar ba mu Naira 8,000 ga kowane iyali tare da ba wa kan su N70bn.
“Mun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai da ta biya dukkan bukatunmu, sannan ta fara wani mataki na kasa baki daya daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta, 2023 domin tilasta wa gwamnati ta sauya manufofinta na yaki da talakawa da ma’aikata,” in ji sanarwar.