
A karshe dai an mika jerin sunayen ministoci ashirin da takwas da za su kafa majalisar ministocin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ga majalisar dattawa, biyo bayan raɗe-raɗi da aka rika yi na tsawon makonni.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa gwamnan jihar Rivera, Nyesom Wike, wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP, ya shiga jerin sunayen ministocin na Tinubu da aka karanta a zauren majalisar dattawa a yau Alhamis.
Tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi; tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i; da mai magana da yawun shugaban kasa, Dele Alake shi ma ya sanya jerin sunayen.
Bayan dogon jiran da ‘yan Najeriya suka yi, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, a yau Alhamis, ya gabatar da jerin sunayen ministocin Tinubu a gaban majalisar dattawa domin tantancewa.
Gbajabiamila, wanda shi ne tsohon kakakin majalisar wakilai, ya gabatar da jerin sunayen ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da misalin karfe 01:19 na rana.
Daga nan ne Akpabio ya karanta jerin sunayen ministocin 28.
Ga sunayen :
– Abubakar Momoh
– Ambassador Yusuf Miatama Tukur CON
– Arch. Ahmed Dangiwa
– Barr. Hannatu Musawa
– Chief Uche Nnaji
– Dr. Berta Edu
– Dr. Dorris Aniche Uzoka
– H.E. David Umahi
– H.E. Nyesom Wike
– H.E. Badaru Abubakar CON
– H.E. Nasiru Ahmed El-Rufai
– Rt. Hon. Ekperipe Ekpo
– Hon. Nkiru Onyeojiocha
– Hon. Olubunmi Tunji Ojo
– Hon. Stella Okotette
– Hon. Uju Kennedy Ohaneye
– Mr. Bello Muhammad G.
– Mr. Dele Alake
– Mr. Lateef Fagbemi SAN
– Mr. Muhammad Idris
– Mr. Olawale Edun
– Mr. Waheed Adebayo Adelabu
– Mrs Iman Suleiman Ibrahim
– Professor Ali Pate
– Professor Joseph
– Senator Abubakar Kyari
– Senator John Eno
– Senator Sani Abubakar Danladi