Home Labarai Juyin-mulkin Nijer: Zanga-zanga ta ɓarke a Yamai

Juyin-mulkin Nijer: Zanga-zanga ta ɓarke a Yamai

0
Juyin-mulkin Nijer: Zanga-zanga ta ɓarke a Yamai

Ɗaruruwan mutane su ka yi cincirindo a gaban ginin majalisar ƙasar da ke Yamai, domin nuna goyon baya ga sojoji.

Masu zanga-zangar sun buƙaci Rasha ta kawo masu ɗauki, tare da roƙon dakarun tsaron Faransa da su janye daga ƙasar.

BBC ta rawaito cewa wasu masu zanga-zangar na ɗauke da tutar Rasha. Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna wani yunƙurin shiga tsakani da Rasha ta yi.

Masu zanga-zangar sun cinna wa ofishin jami’iyar PNDS Tarayya wuta, wadda kuma ita ce jam’iyar hamɓarraen shugaban ƙasar.

An jinkirta zanga-zangar nuna goyon bayan ga sojoji ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka tabka a Yamai din.

Ra’ayoyin ƴan ƙasar ya banbanta, inda wasu ke ganin juyin mulkin abu ne marar kyau, wasu kuma na ganin matakin ya yi daidai.

A ranar Laraba, ɗaruruwan magoya bayan shugaba Mohamed Bazoum, sun yi zanga-zangar adawa da matakin sojin ƙasar, sai dai dakarun tsaro sun tarwatsa su da harbin bindiga.

Magoya bayan shugaba Bazoum sun ce ba za su amince da juyin mulkin ba, sai dai babu tabbacin hanyar da za su bi wajen adawa da juyin mulkin.

Rundunar sojin Nijar ta goyi bayan juyin mulkin da sojoji suka sanar a gidan talabijin na ƙasar, inda hakan ke nuna haɗin kai tsakanin dukkan rundunonin tsaron ƙasar.

Sai dai har yanzu babu tabbacin wanda zai jagoranci gwamnatin sojin.