Home Labarai Bashin N250bn: Dillalan mai sun roƙi gwamnati ta biya su kuɗaɗensu ko su dakatar da ayyukansu

Bashin N250bn: Dillalan mai sun roƙi gwamnati ta biya su kuɗaɗensu ko su dakatar da ayyukansu

0
Bashin N250bn: Dillalan mai sun roƙi gwamnati ta biya su kuɗaɗensu ko su dakatar da ayyukansu

Wata sabuwar wahalar man fetur ka iya Kunno kai a wasu sassan ƙasar nan matuƙar hukumar NMDPRA ta gaza biyan sama da Naira biliyan 250 kuɗin dakon mai da Kungiyar Dillalan mai Masu Zaman Kansu na Arewa ta ce ta na bi sama da shekara ɗaya.

Ƙungiyar, wacce take da rassa a defo-defo tara da suka haɗa da Kano, Kaduna, Suleja, Minna, Jos, Maiduguri, Gombe da kuma Yola, ta ce rashin biyan ta kuɗaɗen na neman jefa mambobin ta cikin mawuyacin hali.

A wani taron manema labarai da ƙungiyar ta yi a jiya Alhamis a jihar Kano, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Musa Yahya Maikifi ya ce rashin biyan su bashin ya sanya da yawa daga mambobin ƙungiyar sun rasa jarin da za su saro man fetur su kawo shi yankin Arewacin Nijeriya su sayar kamar yadda su ka saba a da.

A cewar sa, akwai makudan kuɗaɗe da kungiyar ke bi da suka maƙale a rusashshen asusun bai-ɗaya na kuɗaɗen man fetur, da aka fi sani da Petroleum Equalization Fund.

Ya koka da cewa bayan an kafa NMDPRA a matsayin sabuwar hukumar da za ta riƙa biyan su kuɗaɗen na dako, akwai sama da Naira biliyan 250 da ta gaza biyan su, wanda a cewar Maikifi, da shi ne za su ƙara jari domin ɗorewar kasuwancin su.

“Rashin biyan mu kuɗaɗen nan ya fara neman durƙusar da mambobin mu. Mu na kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sanya baki a maganar nan ya sa a biya mu.

“Mambobin mu sun fara shiga wani hali domin kasuwancin mu ya fara yin tangal-tangal. Idan ba a biya mu ba, za mu bi hanyoyin da su ka dace don neman hakkin mu. Idan duk da haka aka gaza biyan mu, to fa za mu janye ayyukan mu a yankin arewa kuma yankin zai shiga wani hali na wahalar man fetur,” Maikifi ya yi gargaɗi.