
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta yi watsi da shirin mika mulki ga gwamnatin farar hula a Nijar na shekaru uku.
Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musa ne ya bayyana haka yayin wata hira da BBC a yau Lahadi.
Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban mulkin sojan Nijar, ya bayyana a wani gidan talabijin da a daren jiha Asabar cewa, sojojin kasar za su mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru uku masu zuwa.
Sai dai a cikin hirar Abdel-Fatau Musa ya yi, ya ce wannan mataki na Janar Tchiani wata yaudara ce kawai wajen kawo nakasu a tattaunawa da diflomasiyya.