
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta zargi jami’an tsaron a kan iyakokin Saudiyya da kashe daruruwan bakin haure da masu neman mafaka ƴan kasar Habasha wadanda suka yi kokarin tsallaka kan iyakar Yaman da Saudiyya a tsakanin watan Maris na shekarar 2022 zuwa watan Yunin 2023.
Rahoton na Human Rights Watch mai shafuka 73 a yau litinin ya yi zargin cewa jami’an tsaron kan iyakar Saudiyya sun yi amfani da bama-bamai wajen kashe bakin haure da dama tare da harbe wasu bakin haure da bindiga.
Mutuwar ta hada da mata da yara da dama, a cikin wani hari da aka tsara shi.
Rahoton ya ce “Idan aka aikata a matsayin wani bangare na manufofin gwamnatin Saudiyya na kisan ‘yan ci-rani, wadannan kashe-kashen da ake ci gaba da yi, za su kasance laifin cin zarafin bil’adama.”
Kungiyar da ke sa ido ta yi kira ga kasashen da abin ya shafa da su matsa lamba don ganin an hukunta su sannan kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi bincike.
Binciken da HRW ta yi a baya-bayan nan ya nuna cewa ana ci gaba da kashe-kashen.
Shaidun gani da ido sun shaida wa masu fafutukar kare hakkin bil adama game da gawarwakin da aka gani a kan hanyar su ta yin hijira.
“Lokacin da jami’an tsaron Saudiyya suka ga gungun ‘yan ci-rani, sai suka afka musu da harbe-harbe,” in ji daya daga cikin wadanda suka tsira, a cewar HRW.
Masu neman mafaka da bakin haure sun ce hanyar yin hijira tsakanin Yemen da Saudiyya na cike da cin zarafi da kuma karkashin ikon masu safarar mutane.