
A jiya Lahadi ne Sanatoci suka bayar da tallafin albashin wata daya da ya kai Naira miliyan 109 ga wadanda hatsarin jirgi mara matuki da sojoji suka kai a ranar 3 ga watan Disamba a Tudun Biri, karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna ya rutsa da su.
Harin da jiragen yaki mara matuki na soja ya yi kuskuren kashe fararen hula 85 da suka taru domin gudanar da bukukuwan addini a cikin al’umma.
Ismail Mudashir, mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ne ya sanar da bayar da tallafin a jiya Lahadi a Abuja.
Ya bayyana cewa Jibrin ya sanar da bayar da tallafin ne a gidan gwamnatin jihar Kaduna a lokacin da ya jagoranci tawagar majalisar dattijai domin jajantawa gwamnatin jihar da al’ummar jihar.
Mudashir ya ruwaito Jibrin na cewa za a aika kudin ne ga gwamna Uba Sani, wanda ya karbi tawagar domin kai wa wadanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa Gwamna Sani ya godewa Sanatocin bisa wannan karamci da suka nuna.