
Kungiyar Marubuta ta Jos ta bayyana wacce ta zo ta biyu a gasar Hikayata ta BBC Hausa da aka kammala kwanan nan, Aisha Sani Abdullahi a matsayin jakadiyar kungiyar.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wani taro na musamman da ta shirya domin taya ta murna da ta zo ta biyu a gasar da gajeren labarin ta mai taken: “Tuwon Ƙasa”, wanda ke nuna irin gwagwarmayar da matan Hausawa ke yi a gida.
Shugaban kungiyar, Abba Abubakar Yakubu, ya ce kungiyar ta ga ya dace su hada kai da wadanda suka yi nasara wajen nuna farin cikinsu da godiya ga Allah bisa nasarar da ta samu a matsayinta na mamba.
Ya ce: “Marubuta dari biyar daga kasashe masu magana da harshen Hausa ne suka shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa.
“Don haka, ga wanda zai kai ga zagayen karshe na gasar babbar nasara ce da ta cancanci a karrama kuma ta karfafa wasu suma su yi kwazo sosai.”
A cewarsa, kungiyar ta kuma yaba wa Rabi’atu Ahmad Mu’azu, wadda ta zama ta 9 a cikin 500 da suka fafata.
“Mambobin kungiyar kuma sun yi farin cikin ganin mambobinmu sun fara yin fice a cikin gida Nijeriya da kuma duniya.
“Mun kuma yaba wa Rabi’atu Ahmad Mu’azu da ta kai matakin kusa da na karshe, inda aka ambato wasu labarai guda 12 da suka yi tsokaci kan al’amuran da suka shafi mata a cikin al’ummar Hausawa, tare da labarinta mai suna: ‘Haƙorin Dariya,” inji Mista Abba.