
Ma’aikatar sufurin jiragen sama, ta ce tana aiki kan tsare-tsare don tabbatar da cewa kamfanonin jiragen sama na kasuwanci da ke aiki a Najeriya sun biya diyya ga fasinjojin da aka yi jinkiri ko soke tashin su daga watan Janairu.
Ministan Sufurin Jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Kasa kan Tsaron Kasafin Jiragen Sama na 2024.
Ya ce ma’aikatar ta kuma shirya fitar da jerin sunayen kamfanonin jiragen da suka haifar da jinkiri ko soke tashi a kafafen yada labarai a kowane mako a wani bangare na kokarin.
“Na kira hukumar jin dadin kwastomomi akan yadda za a rika kyautata musu yayin tashi da saukar jiragen.
“Kuma na fadi a jawabin karshe da na yi a lokacin taron masu ruwa da tsakin mu a Legas da kuma taron wayar da kai a Warri.
“Na ce a mako-mako, da fatan za a buga jerin kamfanonin jiragen sama waɗanda ba sa tashi a lokacin da ya kamata, soke tashin jirage, jinkirin jirage, sa’o’i nawa aka jinkirta,” in ji shi.
Keyamo ya kara da cewa: “Ga kowane bata lokaci, akwai rahoto, ainihin rahoton da hukumar ta bayar, me suka yi? sun biya diyya?