
Gwamnatin jihar Kano ta ce umarnin rufe asusunta kan Russia da wasu mutane su ka karbo da ga wata babbar kotun Abuja karya ne.
Gwamnatin ta tabbatar da hakan a yau Laraba a Kano cewa har yanzu tana ci gaba da amfani da asusun nata daban-daban domin gudanar da ayyuka a jihar.
Hakan ya fito ne daga bakin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Isa Dederi.
Dederi ya tabbatar wa manema labarai cewa, babu yadda za a yi Kotu mai hurumi ta zauna a kan hukuncin da ta yanke wanda kuma aka daukaka kara a kai.
Ya ce bisa ga sanarwar ne gwamnatin jihar Kano ta shigar da kara a kan hukuncin ladabtarwa da diyya ta Naira biliyan 30 da mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke.
Hukuncin ya kasance goyon baya ga kungiyar masu Shagunan Masallacin Ido a madadin wadanda abin ya shafa.
Isa-Dederi ya yi mamakin ta yaya kotun da ba ta da hurumi za ta yanke hukunci a Kano.
Mista Isa-Dederi ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta shigar da kara ne saboda babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraren karar, inda ya ce ta ta’allaka ne da mallakar kadarorin tun da farko kuma an mika dukkan bayanai aka yi a kotun daukaka kara.