Home Labarai Kasafin Naira tiriliyan 1.57 yayi kaɗan ga ma’aikatar tsaro — Minista

Kasafin Naira tiriliyan 1.57 yayi kaɗan ga ma’aikatar tsaro — Minista

0
Kasafin Naira tiriliyan 1.57 yayi kaɗan ga ma’aikatar tsaro — Minista

Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya roki Majalisar Tarayya da ta kara kasafin kudin ma’aikatarsa ​​na 2024, inda ya ce Naira Tiriliyan 1.57 da aka ware mata ba za ta isa a yaki rashin tsaro a kasar ba.

Ministan ya yi wannan kiran ne a jiya Larabar lokacin da ya gurfana gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar kan tsaro domin bayani kan kasafin kudin shekarar 2024 na ma’aikatar.

Badaru ya ce hauhawar farashin ayyuka da kuma karin farashin man dizal da man fetur ne ya sa ya yi kira da a kara yawan kason da ma’aikatar ke samu.

Sai dai ministan tsaron kasar ya ce wannan kason bai isa a yaki rashin tsaro ba.

“Ina kira ga Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai da su sake duba kasafin kudin ma’aikatar bisa la’akari da yanayin tattalin arzikin da ake ciki domin baiwa ma’aikatar damar yin aiki yadda ya kamata.

“Kun riga kun san halin hauhawar farashin kayayyakin aiki da tsadar dizal, man fetur, da kuma farashin ayyuka. Kudaden gudanar da ayyuka banza su isa ba kuma muna rokon ku da ku ba mu goyon baya don ganin yadda za mu inganta kudaden da ake kashewa,” inji shi.

Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce ba za a samu hujjar kashe makudan kudade ga ma’aikatar ba idan har ba a samu ci gaba a harkar tsaro a fadin kasar ba.

Ya ce ya zama wajibi a tabbatar da yadda kudaden da aka ware wa ma’aikatar ke inganta tsaro.