
Farfesa Zacchaeus Adangor ya yi murabus daga mukamin kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin jihar Rivers.
A cikin wasikar murabus dinsa mai kwanan wata 14 ga Disamba, 2023, Adangor ya shaidawa gwamna Similanayi Fubara cewa ya fice daga majalisar kwamishinonin a bisa raɗin kan sa.
Adangor, wanda yayi aiki a gwamnatin da ta shude ta Nyesom Wike, wanda Fubara, ya gada, ya gode wa gwamnan bisa ganin ya cancanci a nada shi a muƙamin.
Rikicin da ke tsakanin Fubara da ubangidansa na siyasa, ya yi ƙamari matuka bayan da gwamnan ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2024 ga majalisar dokokin jihar mai mutane hudu da ke biyayya gare shi, sa’o’i bayan ruguza majalisar, wanda ‘yan majalisar 27 da ke goyon bayan Wike suka fice daga jam’iyyar PDP.
An ruguje harabar majalisar da ke zaman tsakiyar rikici tsakanin bangarorin biyu na majalisar da sanyin safiyar jiya Laraba.
Rushe ginin ya biyo bayan umarnin wata babbar kotu da ke Fatakwal wadda ta amince da Edison Ehie, shugaban majalisar jihar mai mutane hudu masu biyayya ga gwamnan a matsayin babban kakakin majalisar dokokin jihar Ribas.