
Kotun koli ta tabbatar da tuhumar cin amanar kasa da ake yi wa shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu.
Tun da fari, gwamnatin tarayya ta roki kotun da ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, inda ta yi watsi da zargin cin amanar kasa da ake yi wa Kanu tare da bayar da umarnin a sake shi bisa hujjar cewa an dawo da shi kasar ba bisa ka’ida ba bayan ya tsallake beli.
Kanu ya na son kotun koli ta amince da hukuncin kotun daukaka kara tare da tabbatar da sallamarsa da kuma wanke shi.
Lauyan gwamnatin tarayya, Tijani Gazali, SAN, ya bukaci kotun koli “ta ba da damar daukaka kara, ta yi watsi da hukuncin kotun da ke kasa, sannan ta tabbatar da hukuncin kotun shari’a (Babban Kotun Tarayya), da cewa wanda ake kara ya kamata a gurfanar da shi a gaban kuliya dangane da tuhumar da kotun da ke kasa ta yi watsi da shi.”
Mista Gazali ya kuma bukaci kotun da ta yi watsi da karar da Kanu ya shigar.
A nasa jawabin, Lauyan Kanu, Mike Ozekhome, ya bukaci kotun da ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar a gabanta tare da mutunta karar da aka shigar domin yin adalci kan wannan lamari.”
Ya bukaci kotun da ta tabbatar da karar da wanda yake karewa ya shigar.
Hukuncin da mai shari’a Garba Lawal ya rubuta ya karyata tare da yin watsi da hukuncin kotun daukaka kara da a watan Oktoban shekarar da ta gabata ta bayar da umarnin sakin Kanu tare da soke tuhume-tuhumen ta’addancin da ake yi masa.