Home Labarai Da yiwuwar mu rufe gidajen mai saboda matsalolin da muke fuskanta — IPMAN

Da yiwuwar mu rufe gidajen mai saboda matsalolin da muke fuskanta — IPMAN

0
Da yiwuwar mu rufe gidajen mai saboda matsalolin da muke fuskanta — IPMAN

Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta ƙasa, (IPMAN), ta koka game da wasu matsaloli da dama da ‘ya’yanta ke fuskanta wajen samun man da suke sara daga kamfanin mai na ƙasar (NNPCL) su kai gidajen mansu musamman na yankin arewacin ƙasar.

Ƙungiyar ta ce wannan lamarin yana iya haifar da ƙarancin man har da ma rufe gidajen mai da dama.

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Zarma Mustapha, ya shaida wa BBC cewa mafi yawan lokaci man fetur ɗin da suke samu daga NNPCL ba ya kai yawan da suke buƙata lamarin da ya sa suke siyan mai daga depo-depo masu zaman kansu kuma galibi sukan sayi man ne a kan farashi mai tsada wanda yake tasiri kan farashin da suke siyar da man a giajen mansu.

‘Muna cikin wani irin mawuyacin hali, musamman mu da ke arewacin Najeriya. A kudu suna iya ƙara karamar riba a kan farashinsu saboda suna samun sauƙi wurin ɗauko mai daga depo zuwa gidajen mansu.

” Amma mu da muke arewa ba mu iya samun mai a kan farashin da NNPCL take bayarwa daga depo masu zaman kansu, kuma idan zan dauki kayan nan sai na biya kuɗin mota, ga illolin kan hanya, ba karamin nauyi muke ɗauka ba.’ In ji shi.

Ya ƙara da cewa mafi yawan lokaci da kyar suke samun fita a harkokin kasuwanci nasu, kuma idan abubuwa suka ci gaba da tafiya a haka za a kai wani mataki da ba za su iya ci gaba da kasuwancin ba.

Ya ce:’ Idan ba a yi hankali ba, diloli masu zaman kansu za su kasa kasuwancin nasu, su rufe gidajen mansu saboda asara da ake yi da kuma rashin samun mai a kan farashin da ake bukata’.

Mataimakin shugaban kungiyar ya ce dole ne a dauki mataki cikin gaggawa idan har ana son su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu.

BBC Hausa