Home Labarai Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata raɗe-raɗin mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Legas

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata raɗe-raɗin mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Legas

0
Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata raɗe-raɗin mayar da babban birnin Nijeriya zuwa Legas

Gwamnatin shugaba Bola Tinubu ba ta da shirin mayar da birnin tarayya Abuja zuwa jihar Legas.

Ko mayar da wasu ma’aikatun gwamnati daga Abuja zuwa Legas, domin kara inganta aiyukan gwamnati don amfanar ƴan Nijeriya.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

“Muna ganin ya zama dole mu sanar da ‘yan Nijeriya cewa babu kashin gaskiya a cikin raɗe-raɗin da ake ta yi biyo bayan umarnin maida wasu bangarori zuwa Legas da da kuma uwa-uba cewa wai Shugaba Bola Tinubu na shirin mayar da Babban Birnin Tarayya zuwa Legas.

“Wadannan jita-jita, wadanda suka fara fitowa a lokacin yakin neman zabe a shekarar da ta gabata, ‘yan adawar siyasa ne suka dauki nauyinsu na neman kowane irin makamai domin hana Asiwaju Tinubu lashe zaben shugaban kasa a wani sashe na kasar nan.”

A tuna cewa Gwamnatin tarayya ta sanar da mayar da sashin kula da harkokin bankuna na babban bankin Najeriya CBN zuwa jihar Legas.

An samu wannan matsaya tare da tsokaci iri daban-daban daga bangarori daban-daban na al’ummar Najeriya wadanda suke ganin wata boyayyiyar manufa ce ta mayar da fadar mulkin jihar Legas.

“Matsayin Abuja a matsayin Babban Birnin Tarayya na nan daram tunda doka ce ta kafa shi,” in ji Mista Onanuga.