
Daga Hassan Y.A. Malik
Wasu maza guda uku da a ke zargi da yi wa wata yarinya mai shekaru 15 da haihiwa fyade sun shiga hannun ‘yan sanda.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Mista Edgal Imohimi ne ya bayyana wa manema labarai batun kame a ranar Larabar da ta gabata, inda ya ce, wadanda a ke zargin sun fada komar ‘yan sanda ne a ranar 1 ga watan Yuni.
Wannan lamari dai ya faru ne a gida mai lamba 52 da ke a kan titin Jagua, a unguwar Itaketa Imude da ke a yankin Ajangbadi da ke a jihar Legas.
Mutanen 3 sun yi amfani da jan kyalle wajen daure idon yarinyar, tare da yin safararta zuwa dakinsu, sannan suka yi mata layi wajen yin lalata da ita.
A yayin da ‘yan sanda ke gudanar da tuhuma ga wadanda a ke zargin, sun bayyana cewa su ba ‘yan kungiyar asiri bane, amma sun yarda da laifinsu na yi wa yarinyar fyade.
Amma a lokacin da ‘yan anda ke gudanar da bincike a gidansu, an samu wata sharbebiyar adda da kuma wani jan kyalle wanda da shi ne ma suka rufe fuskar yarinya a lokacin da suka yi mata fyaden.
Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa da zarar ‘yan sanda sun kammala bincikensu za tasa keyar mutanen 3 zuwa gaban kuliya.