Home Labarai Gwamna Zulum ya kirkiro da rijista ga ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu sau 4 a mako

Gwamna Zulum ya kirkiro da rijista ga ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu sau 4 a mako

0
Gwamna Zulum ya kirkiro da rijista ga ciyamomin kananan hukumomi su rika sanya hannu sau 4 a mako

Gwamnnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya umarci sababbin shugabannin kananan hukumomin jihar da su tabbatar sun zauna a yankunansu sannan kuma su rika sa hannu a wata rijista sau hudu a kullum domin tabbatar da zamansu a yankunan.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne a yau Litinin a Maiduguri, lokacin da yake rantsar da sababbin shugabannin da aka zaba su 27.

Zulum ya kuma umarci ma’aikatar kananan hukumomin jihar da ta samar da na’urorin daukar hoton bayanan mutane a dukkanin kananan hukumomin domin ciyamomin su rika yin rijista sau hudu a kullum domin tabbatar da cewa suna nan a yankunansu.

Shugabannin za su rika yin rijistar ne da karfe 8 na safe da 12 na rana d 2 na rana da kuma karfe 3:30 na yamma.

Ya ce daukar matakin ya zama dole domin maganin ki ko guduwa daga wurin aiki ba tare da wani dalili mai karfi ba, inda ya jaddada cewa barin wajen aiki ba dalili mai kwari laifi ne na tube shugaba.