
Ƴan bindigar da suka yi garkuwa da mazauna yankin Kuduru su bakwai a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja a ranar 28 ga watan Disamba sun bukaci a biya su Naira miliyan 290 na kudin fansa da kuma maganin tari da kayan abinci domin su sako mutanen da su ka yi garkuwa da su.
Wadanda abin ya shafa da suka hada da mace mai juna biyu da yara uku da manya hudu yanzu sun shafe wata daya da kwana hudu a hannun masu garkuwa da mutanen.
Wani mai faɗa a ji garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ƴan bindigar sun yi barazanar kashe biyu daga cikin wadanda ke hannun na su matukar ba a biya musu bukatunsu kan lokaci ba.
Ya ce masu garkuwar sun kuma bukaci kayan abinci da magunguna da zanin gado da rigunan sanyi.
“Sun tuntube mu mu kawo Naira miliyan 290 domin a sako su ko kuma su kashe biyu daga cikinsu. Muna da mace mai ciki da ’ya’ya uku a cikinsu.
“Sun kuma nemi mu basu maganin tari, bubunan shinkafa da indomie da mafi gina da zannuwan gado da kuma rigunan sanyi.
“Sun kuma ce tilas mu biya su Naira miliyan 290 idan har muna son su sako mana mutanen mu,” in ji shi.
Ya kuma roki Sufeto-Janar Ƴansanda,
Kayode Egbetokun da Shugaban Sojojin Nijeriya, Taoreed Lagbaja da su taimaka su kuɓutar da mutanen da gaggawa.