
Wasu tarin mata, masu sana’ar Gurasa sun yi zanga-zangar lumana a jihar Kano bisa hauhawar farashin fulawa.
Masu Gurasa sun yi zanga-zangar ne a unguwar Chediyar Yangurasa da ke Karamar Hukumar Dala a jihar Kano a yau Juma’a, inda su ka ce yanayin na neman raba su da sana’ar su tun ta kakanni.
Da ta ke yi wa manema labarai jawabin dalilin yin zanga-zangar, shugabar masu gashin gurasa ta Jihar Kano, Fatima Auwal ta ce sun gudanar da zanga-zangar ne sakamakon hauhawan farashin fulawa.
A cewar ta, kullum su ka je siyan fulawa sai sun samu ta kara farashi da a kalla N1,500.
Ta ce tun buhun fulawa yana Naira dubu 16 suka fara zanga-zanga amma gashi yanzu suna siyan sa Naira dubu 43.
“Ya za mu yi da ran mu. Kullum sai an kara mana farashi. Fiye da rabin mu sun daina sana’ar Gurasa kuma ita kadai muka iya a duniyan nan.
“Da fulawar IRS mu ke amfani saboda ta fi mana inganci da dadin aiki. Saboda haka muna kira ga Abdussamad BUA da gwamnatin tarayya da su shiga wannan lamari su kawo mana ɗauki,” in ji ta.
Fatima ta ce lamarin ya haifar musu da wahala da kuncin rayuwa, inda ta ce dakyar su ke iya ciyar da kansu da daukar nauyin rayuwar ƴaƴansu.
Ta kuma yi barazanar cewa za su tafi yakin aikin sai-baba-ta-gani matsawar aka ci gaba da tafiya a haka.