Home Labarai Dan shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahiafinsa ya bari

Dan shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahiafinsa ya bari

0
Dan shekaru 37 ya yanka mahaifiyarsa akan dukiyar gadon da mahiafinsa ya bari

Daga Hassan Y.A. Malik

Wani matashi mai shekaru 37 da haihuwa da aka bayyana sunasa da Nuruddeen a ranar Larabar da ta gabata ya yi wa mahaifiyarsa mai shekaru 65 yankan rago.

Nurudden Bakare ya aikata hakan ne ga mahaifiyarsa Bosede da ake yi wa lakabi da Iya Fali wannan aika-aika a unguwar Oremeji Ilasamaja da ke a yankin Mushin, jihar Legas, sakamakon zargin mahaifiyar tasa da yin zaman dirshan akan gadonsa da mahaifinsa ya bar masa.

A ranar da abun ya faru, Nuruddeen ya fada cikin zazzafan jayayya da mahaifiyarsa akan sai ta bashi gadonsa, inda da gardama ta yi gardama, nan take Nuruddeen ya dauki wuka ya daba wa mahaifiyrsa a ciki, bayan ta fadi kuma ya yanka makogwaronta kamar dai yadda ake yanka dabba.

Wata shaidar gani da ido da aka bayyana sunanta da Iya Bose, ta bayyana cewa ta jiyosu suna cacar baki, amma ba ta dauka har abin zai kai ga kisa ba.

“Mun jiyo su suna gardama a cikin shagonta kamar dai yadda suka saba, amma sam bamu damu ba saboda dama sun saba irin haka, bamu yi aune ba kawai sai muka ga ya fito jina-jina daga hannunwansa zuwa suturarsa kuma yana fadin na kasheta.”

“Hakan ya sanya muka garzaya zuwa shagonta inda muka isketa tana shure-shure. Ya daba mata wuka a cikinta da kirjinta sannan kuma ya yanke makoshinta. Bana jin wanda ke da lafiyar kwakwalwa zai aikata wannan aiki ga mahaifiyarsa,” inji Iya Bose

Rundunar ‘yan sanfdan jihar Legas ta bakin kakakinta, Sufurentandan ‘yan sanda Chike Oti ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa tuni dai aka kama Nuruddeen aka mika shi ga sashen kisan kai na rundunar da ke a yankin Yaba.