Home Labarai Gobara ta ƙone shaguna 37 a kasuwa a Kano

Gobara ta ƙone shaguna 37 a kasuwa a Kano

0
Gobara ta ƙone shaguna 37 a kasuwa a Kano

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce gobara ta kone shaguna 37 a unguwar Zawaciki da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 01:37 na safiyar yau Laraba.

A cewar Abdullahi, “Mun samu kiran waya da misalin karfe 01:37 na safe daga wani Malam Baba cewa an samu tashin gobara a Zawaciki.

“Mun yi gaggawar tattara jami’an mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 01:47 na safe, muka kashe gobarar domin kada ta bazu zuwa wasu shaguna,” inji shi.

Mista Abdullahi ya ce shagunan 37 din da suka kome sun kasance a kasan bene ne na wani rukunin ginin shaguna.

Ya kuma kara da cewa wasu shaguna uku kuma basu kone kurmus ba kamar sauran.

Ya ce ba a samu asarar rai ba, amma ana kan binciken musabbabin tashin gobarar.