
A jiya Laraba ne ƴansanda suka gabatar da wani matashi mai shekaru 20 mai suna Monday Ojo a gaban wata kotun majistare ta Ado-Ekiti bisa zargin haura gida da kuma satar tukunyar miya da sauran kayayyaki.
Wanda ake kara, wanda ba a san adireshin sa ba, na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume biyu na sata da haura gida.
Sai dai ya musanta aikata laifin.
Dansanda mai shigar da kara, Insp Moyosola Adesola, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 14 ga watan Maris da rana a kan hanyar Falegan, titin Ilawe, Ado-Ekiti.
Adesola ya yi zargin cewa wanda ake tuhumar ya shiga gidan wata Misis Modupe Ajala inda ya sace miya, ‘fufu’, taliyar Indomie, gishiri da albasa, da kudin su ya kai N300,000.
Ta ce laifukan sun ci karo da sashe na 322 da 302(1) (a) na dokokin laifuka na jihar Ekiti, 2021.
Alkalin kotun, Misis Taiwo Ajibade, ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira dubu 50,000 tare da mutum daya da zai tsaya masa.
Ta dage sauraron karar har sai ranar 23 ga watan Afrilu domin sauraren karar.