Home Labarai Ɗalibai biyu sun rasu wajen turmutsutsun karɓar tallafi a jihar Nassarawa

Ɗalibai biyu sun rasu wajen turmutsutsun karɓar tallafi a jihar Nassarawa

0
Ɗalibai biyu sun rasu wajen turmutsutsun karɓar tallafi a jihar Nassarawa

Akalla dalibai mata biyu na jami’ar jihar Nassarawa da ke Keffi ne suka mutu sakamakon wani turmutsutsu da aka yi a wajen karbar kayan tallafi na gwamnati a dandalin taro na jami’ar da safiyar yau Juma’a.

Gwamnatin jihar Nassarawa dai ta yi amfani da dandalin taron da ke jami’ar ne wajen raba kayan tallafin wahalar rayuwa ga daliban jami’ar.

Wani dan jarida da ya shaida yadda al’amarin ya faru ya fada wa BBC daliban matan da suka rasu na daga cikin wadanda suka je neman tallafin.

Mataimakain gwamnan jihar ta Nassarawa, Emmanuel Akadeh wanda ya je jami’ar domin jajantawa dangane da faruwar al’amarin ya ce faruwar al’amarin na da takaici kuma “za mu kafa kwamitin da zai binciko hakikanin abin da ya faru.

BBC Hausa