
Yan bindiga sun sako ‘yan makaranta 286 da aka sace daga makarantarsu da ke Kuriga a jihar Kaduna.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an sace yaran ne a ranar 7 ga watan Maris daga makarantarsu da ke garin Kuriga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna, inda ƴan ta’addan suka yi garkuwa da su zuwa cikin daji.
Sai dai babu tabbas ko an biya kudin fansa kafin a sake su.
Gwamnan jihar Kaduna ya sanar da sakin daliban ne a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a yau Lahadi.
“Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, ina sanar da cewa an sako yaranmu na makarantar Kuriga.
“Muna godiya ta musamman ga mai girma shugaban mu, Bola Ahmed Tinubu, GCFR kan yadda ya ba da fifiko kan tsaro da tsaron ‘yan Nijeriya da kuma tabbatar da ganin an sako yaran makarantar Kuriga da aka sace ba tare da wani lahani ba.
“Yayin da yaran makarantar ke tsare a wajen ƴan bindiga, na yi magana da Shugaban kasa sau da yawa. Ya nuna mana bakin cikinsa kuma ya rarrashe, sannan yana aiki dare da rana tare da mu don tabbatar da dawowar yaran lafiya.
“Muna godiya ga dukkan ƴan Najeriya da suka yi addu’ar Allah ya dawo da yaran makaranta lafiya, wannan ranar farin ciki ce, mu na godewa Allah Madaukakin Sarki,” in ji sanarwar