Home Kanun Labarai Addu’a Abiola yake bukata ba lambar girma ba – Bashir Tofa

Addu’a Abiola yake bukata ba lambar girma ba – Bashir Tofa

0
Addu’a Abiola yake bukata ba lambar girma ba – Bashir Tofa

Tsohon dan takarar Shugaban kasa a rusasshiyar jam’iyyar NRC a zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993, Alhaji Bashir Othman Tofa ya bayyana cewar lambar girma ta GCFR da Shugaba Buhari zai baiwa Moshood Abiola ba tada wani amfani.

A cewarsa, a yanzu haka adduah Abiola yake bukata ba lambar yabon da ba zata amfane shi ba. A ranar 6 ga watan Yunin nan ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Demokaradiyya a Najeriya.

Shugaban ya ayyana wannan ranar ne domin tunawa da zaben da aka hakkake cewar an zabi Moshood Abiola tare da Babagana Kingibe a matsayin Shugaban kasa da mataimakinsa, inda daga isa Gwamnatin Janar Babangida ta wancan lokacin ta soke zaben.

A wata wasika da ya aikowa da DAILY NIGERIAN, Alhaji Bashir Tofa ya bayyana cewar ayyana ranar zaben nan a matsayin ranar demokaradiyya ako baiwa Abiola lambar girma ta GCFR ba tada wani amfania gare shi.